Tsohon dantakarar mataimakin gwamnan yayi kira ga tsaffin gwamnonin da su hada kawunansu don ci gaban jihar.
Murtala Sule Garo ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wajen taron tsofaffin ‘yan majalisar dokokin jihar Kano na 8 da 9 da aka yi a jihar a ranar Talata.
“Abin takaici ne ganin jihohi kamar Zamfara, wacce ba ta kai Kano ci gaba ba, amma suna samun ci gaba saboda tsofaffin gwamnoninsu sun hada kai suna bayar da gudunmawa.
“Amma na nan Kano, ba sa haduwa don tattauna matsalolin da suka shafi jihar.” Inji shi.
Garo ya yi kira gare su da su fifita muradun Kano a kan bambance-bambancen dake tsakaninsu na siyasa, idan da gaske suke, ya kuma ce, ya kamata su hada kai su yi aiki tare domin ci gabanta.
“Hadin kai tsakanin shugabanni shi ne ginshikin samun nasara.” Inji shi. Kamar yadda Aminiya ta rawaito.
Misalin irin wannan baraka tsakanin tsaffin gwamnonin na Kano shine danbarwar masarautar Kano.
Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun alakanta rikicin ne ga Ganduje da kuma Kwankwaso, wanda ci gaban hakan zai kawo babban nakasu ga jihar.
Musamman a yanzu da Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da Al’adu UNESCO ta sa hawan daban da ake yi a jihar a jerin abubuwan al’adu na duniya.
Wanda wannan baraka na iya hana cin gajiyar wannan matsayi yadda ya kamata ta fuskar karuwar tattalin arziki ga jihar.