
Karamar Hukumar Karaye ta kaddamar da shirin dasa bishiyoyi daban-daban ga al’ummar yankin.
Babban Daraktan Kudi da Gudanarwa na Karamar Hukumar Karaye, Alhaji Abdu Mahmuda Doguwa, ya jagoranci bikin a madadin shugaban karamar hukumar, Alhaji Haruna Safiyanu Karaye.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da jami’in yada labarai na karamar hukumar, Karaye Abdullahi Sabo Muhammad ya fitar a ranar Juma’a.
Alhaji Abdu Mahmuda ya kuma yi karin haske kan muhimmancin shuka bishiyu wajen rage kwararowar Hamada da kuma samar da tsaftataccen muhalli.
A nasa jawabin, shugaban sashin noma da albarkatun kasa na Karamar Hukumar Karaye, Malam Mai Kudi Abdu Kiru, ya bayyana cewa gwamnati ta raba bishiyu dubu goma (10,000) ga al’umma, wadanda suka hada da Darbejiya da Rimi da Madaci da Dogon yaro da Dorawa, da sauran su.
“Taron bikin ya samu halartar kafatanin shugabanin karamar hukumar da kuma shugabannin gargajiya da kuma kungiyoyi masu zaman kansu da kuma sauran jama’ar gari.” In ji shi.