Wannan bayanin na kunshe cikin wani rahoto hukumar tattara haraji ta tarayya ta tattara, wanda kuma jaridar Punch ta samu gani, inda adadin ya bayyana an samu karuwa kan kudin shigar idan aka kwatanta da watanni ukun farkon shekarar 2024.
A cewar hukumar samun karin harajin baya rasa nasaba da yadda gwamnatin tarayya ta fara tafiya da zamani a batun samun kudaden shiga wanda hakan zai taimaka wajen ci gaba da samun aiwatar da manyan ayyuka ga yan kasa.
Wannan kudi dai an tsara za a dinga kasafta shi tsakanin bangarorin gwamnati guda uku da suka kunshi gwamnatin tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomi, inda gwamnatin tarayya ke da kaso 15, ragowar 85 kuma jihohi su kasafta da kananan hukumomi a tsakaninsu.
