
Jarumi Vijay tare da malaman da ya gayyata shan ruwa a garinsu
Jarumin bai bayyana cewa ya musulunta ba, ba kamar yadda ake yadawa sakamakon taron da yayi da musulman na jihar ba.
Fitaccen jarumin finafinan Tamil Thalapathy Vijay da aka fi sani da Mai Adda a finafinan ”yan Madras fassarar Hausa ya yi sallah da kuma buda baki da musulmai a Indiya.
Fitaccen jarumin da ya tsunduma harkar siyasa ya yi buda baki da yin sallar Magariba da musulman ne a filin taro na YMCA a aron Royapettah a jihar Chennai ta kasar Indiya a ranar Juma’a.
Kafofin yada labarai na kasar sun rawaito cewa Limaman manyan masallatai 15 ne na fadin jihar Chennai ya gayyata zuwa taron buda bakin tare da kimanin sauran al’ummar Musulman jihar 3,000 .

Duk da cewa bai taba amsa cewa shi musulmi bane, Jarumi Thalapathy Mai Adda ya dauki azumin wannan rana sannan kuma aka sha ruwa da shi a wurin taron.
Ya kuma iso wurin kafin faduwar rana sanye da fararen kaya da kuma farar hula.
Bayan kiran sallah, shi ma ya yi buda baki da dabino da kuma abin sha ya kuma shiga sahu aka yi sallar Magriba da shi.
Taron buda bakin jam’iyyarsa Tamialaga Vettri Kazhagam ce ta shirya shi a kokarin da ta ke na samun karbuwa da kuma wanzar da akidar kasa daya al’uma daya ba tare nuna banbancin addini ko al’ada ba.
Mahaifiyar jarumin Hindu ce mahaifinsa kuma Kirista ne. Jarumin ya kafa jam’iyyar ce don yin takara a zaben kasar da za a gudanar a 2026, kuma yake samun goyon bayan jama’ar yankin.