

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB, ta sanar da kama dalibai 14 da shaidar kammala makarantar gaba da sakandire na bogi, a wannan shekarar.
Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyode ne ya fadi hakan, inda ya alakanta manyan makarantu da taka rawa gurin yaduwar cin hanci da damfara a fannin ilimin kasar nan.
Sai dai masani a fannin ilimi daga jami’ar Bayero, Farfesa Ahmad Iliyasu ya ce bai kamata shugaban hukumar JAMB din ya yanke hukunci akan wannan matsala ba saboda wata babu makarantar gaba da sakandiri a kasar nan da ke taimakawa wurin cin hanci.
Ya kuma ce dangane da batun rubuta jarabawar JAMB, kamata yayi a bi hanyoyin da su ka dace ta hanyar amfani da kwararru a bangaren ilimi domin gudanar da ita yadda ta dace.