Injiniya Ahmad Ishaq Bunkure sabon Mai ba gwamnan Kano Sharawa Na Musamman kan ayyuka ya rasu kwana guda da rantsuwar kama aiki.
Injiniyan ya rasu ne a kasar Misira a ranar Laraba inda ya je neman magani.
A wata sanarwa da Mai Magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Laraba, ta bayyana yadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya ji dangane da rasuwar.
Gwamnan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyalan mamacin da ‘yan uwa da abokan arziki da kuma jihar Kano baki daya.
“Hakika rasuwar Injiya babban rashi ce ga a garemu a gwamnatance, la’akari da yadda muke sa ran kwarewarsa da sadaukarwarsa ga aiki za su taimakawa wannan gwamnati wajen cimma manufofinta na ci gaban Kano.” inji sanarwar
Sanarwar ta ci gaba da cewa, labarin rasuwar Injiniyar kwana daya da rantsarwa ta jijjiga jama’ar jihar, musamman abokan siyasa.