Mutane 9 sun rasu yayin da wasu 7 suka jikkata a wani haɗarin mota da ya faru ranar Juma’a a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
Wannan na cikin sanarwar da Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa reshen jihar Borno Usman Muhammad ya fitar a Maiduguri.
Sanarwar ta ce haɗarin ya shafi motoci biyu, inda mutum 8 suka mutu nan take, sannan ɗaya ya rasu a Asibitin Kwararru da ke Maiduguri.
Wadanda suka rasu sun haɗa da maza manya 5, mace 1, yara maza 2 da yarinya 1.
Kwamandan ya ce ana ci gaba da bincike kan musabbabin haɗarin, sannan ya roƙi direbobi su riƙa tafiya da hankali tare da kiyaye dokokin hanya domin guje wa irin waɗannan asarar rayuka.
