
Daga Aisha Ibrahim Gwani
Gwamnatin Tarayya za ta fara karbar haraji daga mata masu zaman kansu.
Hakan na ƙarƙashin sabon tsarin haraji da ake shirin aiwatarwa a ƙasar a sabuwar shekara
Taiwo Oyedele, shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Manufofin Kuɗi da Gyaran Haraji, ne ya bayyana hakan a wani bidiyo da aka wallafa a shafin X a ranar Litinin.
Shugaban ya ce, na cikin hanyoyin samun kuɗi da dokokin haraji ke ɗauke da su.
“Sabon tsarin haraji ba ya bambance tsakanin hanyar halal ko haram wajen samun kuɗi, domin abin da ake dubawa kawai shi ne ko kuɗin ya fito daga wani aiki ko sayar da kaya.
“Ga wani misali idan mace na zaman kanta, wannan aiki ne, kuma hanyar shigowar kudi ce,dan haka suma a dokar harajin ya zama dole su biya.” in ji shi.Wannan matakin na cikin sabon tsarin gyaran haraji da gwamnati ke ƙoƙarin aiwatarwa domin ƙara yawan kudaden shiga da kuma faɗaɗa hanyoyin samun haraji a ƙasar nan.