
Gwamnatin Sojin Nijar, ta sanar da cewa ranar 26 ga watan Yuli za ta zama Ranar ’Yancin ƙasar.
26 ga watan na yuli itace ranar da sojoji suka kifar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum, a shekarar 2023.
Wannan bayani ya fito ne daga wata majiyar kafar watsa labarai ta Air Info Agadez.
Kafar ta ce, gwamnatin sojin ta ayyana ranar ne domin tunawa da juyin mulkin da sojojin suka yi, wanda ya kawo ƙarshen mulkin Bazoum.
Kwamitin ministocin Nijar, ya ce za a gudanar da bukukuwan ranar ta musamman da saukar Alƙur’ani da addu’o’in neman zaman lafiya da albarkar damina wacce za a gudana a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli.
Gwamnatin ta kuma buƙaci jama’ar ƙasar su riƙa yi mata addu’a domin samun zaman lafiya da kuma ci gaba.
An kifar da gwamnatin Bazoum ne a ranar 26 ga watan Yulin 2023, a ƙarƙashin jagorancin shugaban mulkin soja Abdourahmane Tchiani.