Aminu Abdullahi Ibrahim
Daraktan yada labarai na fadar gwamnatin Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana haka ranar Lahadi, yayin bitar kwanaki biyu ga ‘yan Jaridar gidan gwamnatin Kano, wanda gwamnatin Bauchi ta shirya.
Sunusi Bature, ya ce gwamnonin Kano da Bauchi suna da kamanceceniya da juna ta fuskar siyasa da tabbatar da tallafawa al’ummar su a kowane bangare.
Sunusi Bature, ya ce gwamnonin Kano da Bauchi suna da kamanceceniya da juna ta fuskar siyasa da tabbatar da tallafawa al’ummar su a kowane bangare.
A nasa bangaren mai baiwa gwamnan Bauchi shawara kan harkokin yada labarai, Mukhtar Muhd Gidado, ya ce sun shirya taron ne don karawa ‘yan jaridar gidan gwamnati sanin makamar aiki.
Ya kara da cewa irin wannan taruka da suke shiryawa suna ganin canji a yadda ‘yan jaridar ke gudanar da ayyukansu.
Mukhtar Muhd Gidado, ya ce sun zabi jihar Kano don gudanar da taron bitar duba da yanayi mai kyau.
Ya kuma bukaci manema labaran suyi amfani da abubuwan da aka koyar da su wajen inganta aiyukan su na Jarida.
