
Gwamnatin Kano ta sanar da kwace gidajen da ba a kammala aikin su ba a rukunin gidaje na Amana da Kwankwasiyya biyo bayan cikar wa’adin da ta bayar.
Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Gidaje, Arc. Ibrahim Adamu ne ya sanar da haka yayin taron manema labarai a karshen mako.
“Biyo bayan yunkuri gwamnati na samar da kyakyawan yanayi wannan guri, gine gine da aka ci kaso mai yawa wajen ginasu, gwamnati ta kara musu wa’adi zuwa karshen watan Disamba domin kammala su”. In ji shi.
Kwamishinan ya kuma ce, za su rushe dukkanin gine gine da suka saba da ka’idar biranen da aka bayar.
A baya gwamnatin Kano ta bayar da sanarwar dukkanin masu filaye da gidajen da basu kammala ginasu da su dawo su cigaba da aikin gini, su kuma tare kafin cikar wa’adin da ta bayar.