Yaran an makare su ne a cikin wata motar daukar kayan gwari kirar J5 kan hanyarsu ta zuwa jihar Nassarawa ‘yansanda a Abuja suka kama motar da kuma ‘yan rakiyar yaran.
Ma’aikatar Kula Harkokin Mata da Yara da kuma Nakasassu ta jihar Kano ta ce, ta karbi yaran a ranar Asabar daga Abuja.
Daraktar Wayar da Kan Jama’a ta ma’aikatar, Bintu Nuhu Yakasai ce ta bayyana karbar yaran a wata sanarwa.
Kwamishinar ma’aikatar, Amina Abdullahi HOD kuma ta tabbatarwa da Premier Radio hakan a wata hira ta wayar tarho da wakilin tashar.
“Takardar ce aka aiko mana, kuma aka duba aka kuma bincika aka gano cewa yaran nan ‘yan asalin Sumaila ne da aka yi kokarin safararsu a cikin mota domin yin almajiranci ….
“Cikin yardar Ubangiji an dawo mana da su jihar Kano kuma mun kirawo shi shugaban karamar hukumar Sumaila Sumaila Alhaji Farouk Sumaila kuma ya zo ya karbi yaran kuma an tabbatar ‘yan Sumaila ne.
An sa su a motoci bayan sun ci sun sha, mai girma gwamna ya bayar da umarni a yi duk abin da ya kama a yi na yakamata a mayar da su gaban iyayensu”. Inji Kwamishiniyar
A Larabar ne rundunar ‘yansandan Abuja ta kama wata motar daukar kayan gwari kirar J5 dauke da yaran masu shekaru hudu zuwa 12 da wasu mutune suka yi yunkurin kai su jihar Nassarawa a cikin mawuyacin hali.
Rahotanni sun ce, jim kadan bayan kama yaran ne da kuma tsare su a ofishin ‘yan sanda na Abuja, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila ya je domin ya karbo su, don mayar da su gida amma hakan ya faskara.