Hukumar Tara kudin haraji ta jihar Kaduna (KDIRIS) ta rufe wasu bankuna da kamfanoni a jihar a bisa laifin biyan haraji.
Hakumar ta ce ta rufe su ne a bisa harajin da take bin su da ya Kai sama da Naira Biliyan 100.
Bankunan da aka rufe sune Unity Bank da Bank of Agriculture da kuma FCMB da kuma Otal din Hamadala duk a babban birnin jihar.
Wacce ta jagorancin rufe bankunan a karkashin kwamitin kar-ta-kwana na hukumar kuma Lauyar Kamfanin Aisha Ahmad, a hirarta da manena labarai ta ce, hukumar ta dauki wannan mataki ne bayan ta bi duk hanyoyin da suka kamata amma abin ya faskara.