
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba shi takardar kama aiki a ranar Litinin a wani kwarya-kwaryar biki a gidan gwamnati
Wanda aka nada shi ne Umar Farouk Ibrahim wani tsohon ma’akacin gwamnati da ya rike mukamai daban-daban a jihar
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar da dare.
Umar Farouk Ibrahim, ya kwashe sama da shekaru talatin yana aikin gwamnati a inda ya rike mukamai daban-daban a ma’aikatun jihar.
Ciki har da Babban Sakatare a ofishin Sakataren gwamnatin jihar kafin yayi ritaya.
Sanarwar ta ce, gwamnati na fatan zai kawo cigaba sosai a sha’anin tafiyar da harkokin aikin gwamnati bisa kwarewarsa da kuma gogewa.

