Da yake jawabi yayin bude zaman majalisar Karo na 27, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya kawo zaman majalisar sabon gidan gwamnati dake rukunin gidajen Kwankwasiyya ne domin raya birnin da kuma janyo hankalin al’umar da suka mallaki gidaje a birnin domin su tare da iyalansu.
Yace gwamnatin jiha ta samar da dukkanin abubuwan more rayuwa a rukunin gidajen da nufin kyautata rayuwar mazauna yankin.
Idan za a iya tunawa, gwamnatin jihar Kano ta bada wa’adin watanni uku ga wadanda suka mallaki gidaje a birnin Kwankwasiyya da su hanzarta tarewa a gidajensu ko kuma gwamnati ta dauki matakin da ya dace a kan gidajen.
A wani cigaban kuma, gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwarsa bisa karancin ruwa da wasu yankunan birnin Kano ke fuskanta, inda ya umarci dukkanin masu ruwa da tsaki da su gaggauta kawo karshen matsalar cikin hanzari.
