Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin duba Cibiyar ruwa ta Taluwaiwai dake karamar hukumar a ranar Talata.
Ya ce a kokarin cika alkawarin da suka yiwa al’ummar Rano zasu samar da manyan Injina da zasu rinka tacewa da tunkudo ruwa daga cibiyar ruwa ta Taluwaiwai zuwa cikin garin Rano
Ya ce sun samar da kwamiti da zai bibiya tare da tabbatar da kawo karshen matsalar ta ruwan sha.
Abba Kabir Yusuf ya kuma baiwa ma’aikatar albarkatun ruwa umarnin yashe ciyawar da ta mamaye tafkin dake samar da ruwan.
A nasa bangaren kwamishinan ma’aikatar albarkatun ruwa na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya ce gwamnatin Ganduje ce ta sace kayayyakin dake samar da ruwa a cibiyar a baya.
Ya ce tuni suka fara cika umarnin gwamnan na kawo karshen matsalar ruwa a garin na Rano.
Doguwa ya ce sun dauki hanyoyi daban daban na kawo karshen matsalar inda suka fara aikin daga Tiga zuwa Rano.
