
Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan ya bayyana haka ne wajen taron biyan tsoffin kansiloli hakokin su karo na 2 da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano ranar Alhamis.
Abba Kabir ya ce yaga daya daga cikin shugabanin APC da ke gargadin tsoffin kansilolin da cewa kada su ci amanar su.
Gwamnan ya ce rashin Imani da tunani da kuma rashin kishin al’ummar Kano yayi yawa.
Ya kuma kalubalanci shugaban na APC dake cewa 2027 na zuwa.
Ya ce muguntar da gwamnatin Ganduje ta yiwa kansilolin ce Allah ya musanya ta zuwa alkairi.
Ya ce zuwa sati na biyu na watan Nuwamba mai zuwa gwamnati zata kammala baiwa tsoffin kansilolin kudaden su na aiki da suka yiwa gwamnati.