Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa na aiki don inganta samar da ruwan sha da tuka-tuka masu amfani da hasken rana a karamar hukumar Nasarawa.
Gwamnan ya bayyana hakane yayin kaddamar da ayyukan hanyoyi guda biyu masu tsawon kilomita uku da Dan Majalisa mai wakiltar Nasarawa, Hassan Shehu Hussain zai gina a yammacin Lahadi.
Ayyukan guda biyu sun haɗa da gina hanya mai tsawon kilomita biyu a Tudun Murtala da kuma hanya mai tsawon kilomita guda a Hotoron Kudu wanda za a kammala cikin kwanaki 50.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce irin wannan muhimmin aiki zai sauƙaƙa zirga-zirga ga mazauna yankunan.
Ya kuma yi kira ga ‘yan majalisa a kowane mataki su kwaikwayi wakilin na Nasarawa wajen kawo ayyukan ci gaba a yankunansu domin inganta rayuwar al’umma.
Ya ce duk aikin da dan majalisar na Nasarawa zai yi yana neman shawarar gwamnatin Kano domin gudun yin aiki akan aiki, adon haka ya ce yana alfahari da karamar hukumar ta Nasarawa da al’ummar dake cikinta.
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin jajircewar gwamnatin yanzu a fannonin ƙarfafa matasa, samar da ruwan sha mai tsafta, fitilun titin da ake amfani da hasken rana, da hanyoyin sadarwa da sauran su.
Ya kara da cewa kwanan nan zasu fara kwashe kwatami da sanya silaf domin rufe su, sannan zasu gina sabbin tituna da sanya fitilu a karamar hukumar.
Da yake jawabi da majalisar mai wakiltar Nasarawa, Hassan Shehu Hussain, ya ce an gina hanyoyin tun lokacin mulkin farko na Sanata Kwankwaso amma bayan lalacewar su aka yi watsi da su.
Ya ce wannan ne yasa shi daukar alkawarin gina sabbin hanyoyin domin saukakawa al’ummar yankin.
Hassan Shehu Hussaini, ya ce daga zabar sa zuwa yanzu ya gina hanyoyi da asibitici da dama a yankuna daban daban na karamar hukumar Nasarawa.
Ya kuma ce da zarar an kamala Asibitin za a sanya masa suna Abba Gida-gida, yayin da Asibitin da ya samar a Ladanai zai sanya masa sunan matemakin gwamna Kwamaret Aminu Abdulsalam.
