Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sallami Sakataren Gwamnati Baffa Bichi da kuma wasu Kwamishinoninsa a wani garambawul a majalisar zartaswa ta jihar Kano
Abba Kabir Yusuf ya sanar da sauye-sauyen ne a majalisar zartarwar jihar domin aiwatar da daidaita siyasa mai ma’ana a cikin gwamnatin a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnsa Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a ranar Alhamis
Wadanda sauye-sauyen suka shafa sun hada da Shugaban Ma’aikata Alh. Shehu Wada Sagagi, wanda aka rushe ofishinsa da kuma Sakataren Gwamnatin Jihar da Dakta Abdullahi Baffa Bichi wanda aka cire bisa dalilai na lafiya
Wadanda suka ci gaba da riƙe mukamansu sun hada da Babban Lauyan Jiha kuma Kwamishinan Shari’a Barista Haruna Isa Dederi da Kwamishina Noma da Dakta Danjuma Mahmoud da Kwamishinan kuma Kwamishinan Lafiya Dakta Abubakar Labaran.
Sauran sune Kwaishinan Kasa da Tsare-Tsare Honorabul Abduljabbar Mohammed Umar da Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare, Honorabul Musa Suleiman Shannon da Kwamishinan Ayyuka da Gidaje Injiniya Marwan Ahmad.
Haka ma Kwamishinan Albarkatun Kasa da Ma’adinai Sefiyanu Hamza da Kwamishinan Harkokin Addini, Shiekh Ahmad Tijani Auwal da Kwamishinan Matasa da Wasanni da Honorabul Mustapha Rabiu Kwankwaso da Kwamishinan Zuba Jari da Kasuwanci Adamu Aliyu Kibiya da kuma Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Ayyuka na Musamman Janar Mohammad Inuwa Idris Mai ritaya