
Ɗan marigayi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, ya gode wa shugaba Bola Tinubu da kuma daukacin ‘yan Najeriya tare da nuna farin cikinsa kan yadda aka karrama mahaifinsa ta hanyar yi masa jana’izar ban-girma.
Yusuf Buhari ya bayyana hakan ne a taron majalisar zartaswa na musamman da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis domin yi wa Buhari addu’o’I da kuma alhinin rasuwarsa.
Babban dan marigayin namiji ya halarci taron tare da ƴan uwansa, ya gode wa gwamnatin shugaba Tinubu saboda irin goyon baya da kuma gudunmawar da ya bai wa mahaifinsa da kuma iyalansu.
Ya kuma gode wa majalisar tarayya, gwamnan jihar Katsina Dikko Radda, sauran gwamnoni da kuma ƴan Najeriya saboda taya su alhinin rashin da suka yi