
Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ne ya sanar da ganin watan Azumin Ramadan a ranar Juma’a da dare.
Da yake sanar da ganin watan a fadarsa a Sakkwato, Sarkin Musulmi, ya bayyana cewa an tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan a garuruwan Bama da kuma Maiduguri a Jihar Borno.
Don haka, Asabar 1 ga watan Ramadan 1446 Bayan Hijira, ta yi daidai da 1 ga watan Maris 2025 Miladiyya.
Sanarwar tasa ta zo ne ’yan sa’o’i bayan hukumomin ƙasar Saudiyya sun tabbatar da ganin watan a Ƙasa Mai a ranar Juma’a.
A don haka ranar Asabar, ita ce daya ga watan Ramadan na shekarar 1446, wanda ya yi daidai da daya ga watan Maris din 2025.