An ceto ɗalibai 100 daga cikin 315 da ’yan bindiga suka sace a Makarantar St. Mary’s da ke Papiri a Jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro tare da mafarautan yankin sun bazama cikin dazuzzukan da ke makwabtaka da Papiri domin neman waɗanda aka sace.
’Yan bindigar sun kai farmakin ne a ranar 21 ga Nuwamban 2025, inda suka mamaye makarantar suka tafi da mutum 315 ciki har da ɗalibai guda 303 da kuma malamai guda 12.
A rana ta farko bayan harin yara guda 50 sun yi nasarar tserewa tare da kuma suka koma hannun iyayensu, wanda kuma addadin waɗanda suka rage a hannun ƴan bindigar zuwa mutum 265 kafin wannan sabon cigaba na ceto wasu daga cikinsu.
Gwamnatin Jihar Neja ya bayyana cewa kafin aukuwar lamarin ta samu sahihan bayanan sirri, game da yiwuwar tashin hankulan al’ummar jihar, saboda haka ta dakatar da ayyukan gine-gine tare da rufe makarantun kwana a yankunan da abin ya shafa.
