
Tsohon gwamnan Kano kuma tsohon shugaban jama’iyyar APC, Dr Abdullahi Umar Ganduje , ya karkatar da hannun jarin jihar Kano zuwa kamfanin ‘ya’yansa a wani binciken kwakawaf da jaridar Premium Times ta gudanar’.
A cewar jaridar, binciken nata ya gano cewa kason gwamnatin Kano a Tashar Sauke Kaya Ta Dala (Dala Inland Dry Ports) Ganduje ya karkatar da kashi 20 cikin 100 na kason gwamnatin Kano zuwa wani kamfani mai zaman kansa wanda mallakin ‘ƴa’ƴan sa.
Binciken ya kuma gano cewa kafin ya karkatar da hannun jarin sai da ya saka ‘ya’ƴansa a cikin wannan kamfani tun da farko kafin ya mika wa kamfanin ƴaƴansa wannan kaso, ita jihar kuma sai da ta ji a salansa.
“Hakan da ya yi, ya cire Jihar Kano daga zama mai hannun jari a aiki gaba ɗaya, ya kuma sanya ‘ya’yansa su zama daraktoci da masu wannan hannun jari. Haka kuma ba da jimawa ba Ganduje wanda a lokacin sa ne gwamna, ya ba da kwangilar ayyuka da asali gwamnatin jiha ce ke da alhakin aiwatarwa bisa yarjejeniyar da ka kulla tun farko”. In ji rahoton binciken.
Rahoton ya kuma ce, a ranar 4 ga Satumba 2006, shekara goma kafin Ganduje ya hau mulki, Gwamnatin Jihar Kano ta sayi kaso 20 cikin 100 a tashar (Dala Inland Dry Port Limited) a lokacin gwamnatin tsohon gwamna Ibrahim Shekarau.
Kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu Da Kuma Kungiyoyin Tsimi Da Tanadi Ahmad Yakasai ne, a zamanin mulkin Ibrahim Shekarau ya sanya hannu a yarjejeniyar a wancan lokaci.
PREMIUM TIMES ta gano cewa, a lokacin Ganduje ya na gwamna, ya saka ‘ya’yansa a cikin kamfanin da za su mallaki wannan tasha, ya kuma zaftare kudin jihar har sama da Naira Biliyan 2 ya bayar da kwangilar a gyara tashar domin ta soma aiki.
Ya kuma yi amfani da ikonsa na gwamna a wancan lokacin, ya kuma yi gaban kasa ya mika kason jihar ba tare da bin doka da ka’ida ba zuwa ga wannan kamfani da ya’yansa ke da mallaki.
Babban Darektan Ma’akatar Kasuwanci Da Cinikayya Ta Jihar Kano Bashir Uba, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa lallai jihar Kano ba ta sayar da wa kowa hannun jarinta na tashar Dala ba. Hasali ma a yanzu haka tana binciken yadda aka yi hannun jarin nata yayi batar dabo