
Sanarwar rasuwar ta fito ne daga iyalansa a ranar Talata da dare. Za kuma a yi jana’izarsa yau Laraba a kofar Kudu da misalin 10:00 na safe
Galadiman Kano ya rasu yana da shekaru 92 kuma shi ne dattijo mafi tsufa a duk Masarautar Kano
Alhaji Abbas Sunusi kawu ne ga Sarki Muhammadu Sunusi II, kuma mahaifi ga shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas.
Marigayin shi ne Wamban Kano babban ɗan majalisar Sarki kafin daga likafar sarautarsa zuwa Galadiman Kano.
Tun a shekarun 1950 Abbas Sanusi ya zama mamba a majalisar Masarautar Kano, inda a karon farko mahaifinsa, Sarki Sanusi I, ya naɗa masa rawanin Sarkin Dawakin Tsakar Gida kuma Hakimin Ungogo a shekarar 1959.
A shekarar 1962 kuma Ɗan Iyan Kano a zamanin mulkin Sarki Muhammadu Inuwa, sannan ya zama Wamban Kano a lokacin Sarki Ado Bayero.
A lokacin mulkin Sarki Muhammadu Sunusi II na farko ne aka ɗaga likafarsa zuwa Galadiman Kano.
An haifi Abbas Sanusi a shekarar 1933 a garin Bichi, inda ya soma karatunsa a Makarantar Ƙofar Kudu a shekarar 1944, sannan a shekarar 1948 ya tafi Makarantar Kano Middle School da a yanzu ake kira Rumfa College.