
Aminu Abdullahi Ibrahim
Gamnatin Kano ta ce fiye da ‘yan daba 2000, suka mika wuya domin shiga shirin Tudun Muntsira (Safe Corridor) na gwamnatin Kano.
Kamishinan yada labarai Kwamaret Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana haka a Litinin din nan a babban dakin taro na gidan gwamnatin Kano.
Jawabin nasa na zuwa yayin taron karfafa tsaron kasa ta hanyar hadin kai da cigaba a wani bangare na bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai.
Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce zuwa yanzu karkashin shirin Tudun Muntsira (Safe Corridor) an tantance matasa dake kwacen waya da fadan daba da shaye-shaye fiye da dubu 2000.
Ya kara da cewa abin takaici shine yadda wasu daga cikin wadannan matasa suka fara mallakar bindiga suna amfani da ita a cikin unguwanni.
Sai dai ya ce abin sha’awa shine wasu daga ciki sun dawo da Bindigoginsu don shiga tsarin Tudun Muntsira.
Ya ce sun yi haka saboda yadda da shirin gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da tabbatar da cewa zai aiwatar da alkawarin da ya yi musu.
Waiya, ya kuma ce tun lokacin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya karbi mulki ya tarar da fadan daban siyasa da na unguwanni.
Ya ce wannan ya samu gurin zama sakamakon watsi da matsalar da gwamnatin da ta gabata tayi.
Ya ce itace ta wofantar da rayuwar matasa har matsalar ta girmama sakamakon tallafi da suke samu daga jami’an gwamnati.
Kwamishinan yada labaran Ibrahim Waiya, ya kara da cewa wannan ne dalilin da ya sa gwamnan Kano Abba ya samar da tsarin Tudun Muntsira (Safe Carridor).
Ya ce duk wanda ya yarda cewa zai dena kwacen waya da fadan daba to gwamnan Kano zai tallafa masa.
Da yake jawabi yayin taron Farfesa Muhd Babangida, ya ce dole sai matasa sun shiryu za a samu nagartacciyar al’umma.
Ya ce matasa ne suka taka rawar gani wajen samun ‘yancin kan Najeriya a baya, yana mai bayyana wajabcin shigar da matasa cikin mulki.
Farfesa Muhd Babangida, ya kuma bukaci gwamnati ta yiwa masu sayen rodi rijista don rage sayen karafunan sata da ake yi.
A nasa jawabin sarkin Kano Muhammadu Sunusi ii da ya samu wakilcin Sarkin Dawaki Mai Tuta, Abubakar Bello Tuta, ya bukaci gwamnati ta tashi tsaye musamman yadda dillalai ke sayar da fili da gonaki da gidaje ga mutanen da ba a sani ba.
Ya ce akwai bukatar kawo gyara a lamarin don samun ‘yanci mai cike da zaman lafiya.
Ya kuma bukaci kyautata zumunci a tsakanin al’umma.
Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki da wakilan hukumomin tsaro dake jihar nan.