Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta umarci tsohon shugaban kamfanin mai na NNPCL, Mele Kyari, da ya rinka bayyana a hedikwatar hukumar da ke Abuja kullum, yayin da ake zaton gurfanar da shi a kotu nan gaba.
Kyari na fuskantar bincike kan yadda aka kashe sama da dala biliyan 2.5 wajen gyaran matatun mai guda huɗu na ƙasar nan, duk da cewa har yanzu ba sa aiki.
Majiyoyi sun bayyana cewa Kyari ya riga ya samu beli daga hannun EFCC amma an yi masa sharadin rinka bayyana kullum don bayar da ƙarin bayani da tabbatar da wasu takardu.
Haka kuma, an riga an yi tambayoyi ga tsofaffin shugabannin matatun da wasu manyan jami’an NNPCL tare da ‘yan kwangila.
Akwai yiwuwar Kyari da wasu tsoffin jami’an NNPCL su fuskanci shari’a kan kudaden da aka kashe wajen gyara matatun, ciki har da dala biliyan 1.55 ga matatar mai ta Port Harcourt, dala miliyan 740.6 ga Kaduna, da kuma dala miliyan 656.9 ga Warri.
