Wani mazaunin garin ya ce, jami‘an tsaro sun harbe mutum shida yayin da hukuma ta rushe gidaje kimanin 200 a cewar rahotanni
Wani rikicin ya barke tsakanin al’ummar garin Rimin Zakara dake Karamar Hukumar Ungogo da Jami’ar Bayero da kuma wasu jami’an gwamnatin Kano.
Rikicin ya faru ne a ranar Litinin a yayin jami’an hukumar kula da birane KNUPDA ta je unguwwar domin rushen gidajen da ta ce an yi sub a bida ka’aida ba.
Wasu fusatattun matasan garin sun kone gidan dagacin garin na a bisa zargin yana da hannu wajen a rusan da aka yi.
Wani mazaunin unguwar Baba Habu Mika’ilu wanda kuma shi ne Ma’aji Kungiyar Ci gaban Rimin Zakara ya ce, suna zargin jami’an tsaro sun harbi akalla mutane shida.
Al’ummar garin sun kuma gudunar da sallar al’qanuti domin samun daukin Allah SWT a kan wannan batu.