Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta sanar da kama mutum 398 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a wani babban sumame da aka ƙaddamar domin kawar da masu aikata laifi a fadin jihar.
Farmakin da aka gudanar cikin kwanaki tara ƙarƙashin wata rundunar haɗin gwiwa ta musamman da gwamnatin jihar ta kafa, bisa kulawar rundunar ‘yan sanda.
Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce sumamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka samu wanda ta kai ga kama waɗanda ake zargi a wurare daban-daban na jihar.
Rundunar ta kuma yi nasarar ƙwato wasu makamai masu haɗari da miyagun ƙwayoyi da kuma wayoyin salula guda 29 da aka sace a samamen
Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Rabi’u Muhammad, ya umarci rundunar ta musamman da su ci gaba da zage damtse.
