
Wani matashi dan shekaru 20 da ya kashe mutane ya miƙa kansa ga rundunar ’yan sanda a Jihar Kano sakamako rashin nutsawa da abin ya aikata
Matashin mai suna Abba Umara da ake yi masa inkiyar ‘Abba Dujal’ ya yi ikirarin kashe mutane tare da kwace musu waya ya miƙa kansa ga ‘yan sanda ne sakamakon rashin samun kwanciyar hankali tun bayan ta’addancin da ya aikata a cewarsa.
Kakakin ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya saka murya matashin da hirar da ya yi da shi ya kuma wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.
Da yake amsa tambayoyin Kakakin rundunar, Abba Dujal ya yi iƙirarin aikata manyan laifuffuka da suka haɗa da kisan kai da fashi da makami da kuma satar babur da wayoyin hannu.
Matashin ya yi iƙirarin kashe wani mutum mai suna ‘Boka’ a unguwar Sabon Gari ta Kano, inda ya sace wayarsa Infinix Hot 40i, ya kuma sayar da ita a kan N40,000.
Ya kuma bayyana yadda ya kashe wani mutum a unguwar Kurna da ke Kano, inda ya gudud da wayarsa ƙirar Samsung S26 da ya sayar a kan N160,000.
A jihar Jigawa matashin ya ce, ya kashe wani mutum a Karamar Hukumar Ringim tare da sace babur ɗinsa da ya sayar a N350,000.
Abba Dujal ya c,e yanzu haka ya shekara bakwai bai yi sallah ba. Sai dai ya ce an saka shi a Islamiyya amma malamin ya dawo da shi gida saboda fitinar da yake a makarantar.
A fannin karatun boko kuma, Abba Dujal ya ce, ya taɓa shiga firamare amma daga nan bai ƙara gaba ba.
Aminiya ta rawaito cewa, ya ɗan samu ilimin karatun fatiha da ’yan ƙananan surori a yayin zaman gidan yarin bayan laifin fashi da makami da suka aikata a gidan Hakimin Wudil.
Rundunar ta tabbatar da cewa a halin yanzu, an tsare matashin a sashen binciken manyan laifuffuka domin ci gaba da bincike da kuma tabbatar da gaskiyar iƙirarin da ya yi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar , CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana jin daɗinsa kan matakin da Dujal ya ɗauka na miƙa wuya.