Wani baraon waya ya yi ajalin babban jami’in sojan sama mai suna Laftanar Commodore M. Bubaa ta hanyar soka masa wuka a kirji a jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne ranar Lahadi a gadar Kawo, ta garon Kaduna
Rahotanni sun ce, jami’in ya tsaya domin gyara tayar motarsa da ta fashe yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Jaji, inda yake karatu a Makarantar Horas da Sojoji ta Armed Forces Command and Staff College (AFCSC).
Shaidu sun bayyana cewa yayin da jami’in ke cikin gyara tayar, sai wani mutum ya zo ya buƙaci ya ba shi wayarsa sai Jami’in soja ya ƙi bayar da wayar sai ɓarawon ya ciro wuka ya soka masa a ƙirji.
Wani jami’in sa-kai,mai suna Suleiman Dahiru, wanda ya ga abin da ya faru, ya yi ƙoƙarin kai dauki, amma shi ma ɓarawon ya yanke shi da wuƙa a hannu. Amma mutanen da ke kusa sun kama barawon tare da yi masa dukan kawo wuka har sai da suka hallaka shi.
An garzaya da jami’in sojan zuwa Asibitin Manaal, amma likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
Daga baya an ɗauki gawarsa zuwa ɗakin ajiye gawarwaki na Asibitin 44 Nigerian Army Reference Hospital da ke Kaduna.
Wani babban jami’in soja da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun shiga cikin gari cikin farin kaya domin gudanar da bincike da kuma kawar da masu aikata laifuka a Kaduna.
Kakakin rundunar ’yan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin abin takaici. Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar na ƙoƙarin ƙara tsaurara matakan tsaro a faɗin jihar.
