Rundunar yan sandan jihar Jigawa tace ta samu nasarar kama wani matashi da ake zargi da laifin satar wayar wutar lantarki a karamar hukumar Taura.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar yan sandan, SP Lawan Shi’isu Adam ya fitar.
Ya ce, matashin da ‘yan sanda suka kama suna Adamu Yahaya mai shekaru 27 da haihuwa, dan asalin garin Kwalam ta karamar hukumar Taura.
Sanarwar ta kara da cewa, ana zargin Adamu Yahaya da sace wayar wutar lantarkin wadda gwamnatin jihar ta samu domin gyaran matsalar hasken wutar lantarkin da garin Taura ya shafe shekaru 16 babu wutar lantarki.
SP Lawan Adam ya ce, kwamishinan ‘yansandan jihar, Dahiru Muhammad ya bada umarnin dawo da wannan batu babban sashin binciken manyan laifuka na hedikwatar rundunar yan sandan domin fadada bincike akan sa domin gurfanar dashi a gaban kotu.
