
Jami’ar Bayero ta musanta labarin da ake yadawa cewa ta kori dalibanta sama da 142 dake karatu a jami’ar.
Hakan na cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na jami’ar Lamara Garba ya fitar.
“Labarin dake yawo a shafukan sada zumunta ba shi da tushe ballantana makama don haka jama’ su yi fatali da shi”. In ji shi.
Sanarwar ta kuma yi bayanin gaskiyar abin da ya faru dga wasu dalibanta kan zargin shiga jami’ar da takurdun bogi.
“Daliban da suka nemi shiga jami’ar a shekarar 2022 zuwa 2023 ne suka gano cewa shaidar karatun da suka gabatarwa da jami’ar na bogi ne. Hakan ta sa jami’ar ta kai rahotan takardun bogin ga hukumar shirya jarabawar makarantun gaba da sakandire ta JAMB.” In ji sanarwar
Ta kuma yi hakan ne domin ankarar hukumar yadda wasu daliban ke amfani da takardu suna shiga manyan makarantu domin daukar mataki dakile hakan.
Darakta Lamara Garba ya ce, tuni hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sikandire wato JAMB ta yabawa jami’ar bisa kokarin da tayi na gano masu takardun bogi.