Iyalan tsohon shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha sun gargaɗi Ibrahim Badamasi Babangida kan kokarin bata sunan mahaifinsu.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Muhammad Sani Abacha ya fitar a madadin iyalan marigayin a ranar Lahadi.
Iyalan sun zargi tsohon shugaban kuma aminin mahaifinsu da kirkirar karya a cikin littafinsa mai suna ‘A Journey in Service’.
“Duk wani yunkuri na dora wa Janar Sani Abacha laifin soke zaben wanda a lokacin ya kasance babban jami’in soja a mulkin Babangida, ƙoƙari ne na sauya tarihi da gangan.
“Shekaru da dama, wasu mutane na kokarin bata hakikanin abin da ya faru a wannan lokaci a tarihin dimokuradiyyar Najeriya,” a cewar sanarwar.
Iyalan Abacha sun jaddada cewa a lokacin da aka soke zaben, Janar Abacha ba shi ne Shugaban Kasa ko Babban Kwamandan Askarawan Najeriya ba.
Sun ce Babangida ne, ya ke da cikakken iko, kuma shi kadai ne ke da alhakin duk wani hukunci da gwamnatinsa ta yanke.
“Hukuncin soke zaɓen ya fito ne daga gwamnatin Janar Ibrahim Babangida, wanda yake a matsayin Shugaban Kasa, yana da cikakken iko kuma shi ne ke da alhakin duk wani abu da gwamnatinsa ta aikata,” a cewar sanarwar.
Haka kuma, iyalin Abacha sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji “kagaggun labarai da ake kirkira don karkatar da tunanin jama’a saboda wasu muradu na siyasa ko na kashin kai.”
Iyalan Abacha sun bayyana cewa tsawon shekaru, ana kokarin canza tarihin abubuwan da suka faru a wannan lokaci mai muhimmanci, amma gaskiyar tana nan yadda ta ke.
