
An yi Bikin karbar Dabinon ne a dakin taro na Coronation Hall a gidan gwamnatin jihar a ranar juma’a.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, wanda Sakataren Gwamnati ya wakilta, ya godewa kasar Saudiyya bisa gudunmawar dabinon da ta baiwa jihar Kano.

Yayin da babban jami’i a karamin ofishin jakadancin Saudiyya a Kano, Khalil Admawy, ya wakilci kasar.
A kuma jawabinsa cikin harshen larabci ya ce kasar Saudiyya ta baiwa gwamnatin Kano dabino katon 1,250.

“A wannan shekarar Saudiyya ta baiwa Kano ton 50 na Dabino, Abuja ma ton 50 da sauran jihohin Arewacin kasar nan”. In ji shi.
Khalil Admawy, ya kuma godewa Sarkin Saudiyya Salman Bn Abdulaziz, da Yarima mai jiran gado Muhammad Bn Salman bisa tallafawa musulmi da mabukata a duniya.

Da take jawabi shugabar NEMA Zubaida Umar wacce Jami’in Hukumar Nura Abdullahi ya wakilta, ta yi kira da a tabbatar da cewa tallafin ya isa gurin wadanda aka tsara baiwa.

An raba dabinon ne ga masu bukata ta musamman da kungiyoyin marasa karfi da masallatai da kuma cibiyoyin Addini dake jihar Kano.