Gwamnatin Adamawa ta sauke Lamiɗon Adamawa Alhaji Mustapha Barkinɗo daga matsayinsa na shugaban majalisar sarakunan jihar na dindindin.
Ta Kuma ƙwace ikon naɗawa da warware nadin sarakuna daga hannunsa, inda aka danƙa aikin ga Gwamnan jihar.
Hakan na kunshe ne a wata sabuwar dokar masarautu da majalisar dokokin jihar ta amince da ita a Laraba.
Haka Kuma ta rage ƙasar Masarautar Lamiɗon Adamawa daga ƙananan hukumomi takwas zuwa uku Girei da Jimeta da Kuma Yola.
Shi ma Sarkin Mubi Abubakar Isah-Ahmadu za a rage masa faɗin masarutarsa mai ƙananan hukumomi biyar a ƙarƙashin sabuwar dokar.
Gwamna Ahmadu Fintiri ne ya gabatar da kuɗirin dokar Neman ƙirƙiro sababbin masarautu da naɗa sarakuna a jihar ta Adamawa. Wanda ya takaita ikon sarakunan da Kuma girman kasashensu
Sabuwar dokar masarautun na jiran sa hannun gwamnan jihar ta mayar da shugabancin majalisar sarakunan jihar na karɓa-karɓa tsakanin sarakunan yanka, na tsawon wa’adin shekara guda.
