An rantsar da John Dramani Mahama a matsayin sabon shugaban ƙasar Ghana a wani kayataccen biki a Accra.
Bikin wanda ya samu halartar shugabannin kasashe da yawa an yi shi ne a dandalin Black Star dake babban birnin kasar.
Rantsarwar ta biyo bayan gagarumar nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar da aka yi a watan Nuwamban 2024 bayan ya samu nasara a kan ‘yan takara 12.
Ya kuma lashe baban zaben ne da kashi lashe 56.55 na kuri’un da aka kada a inda ya kayar da Mataimakin Shugaban kasa Mahamudu Bawumia na jam’iyyar NPP mai mulki.
John Dramani Mahama ya taba zama shugaban Ghana a inda ya yi wa’adi daya, yanzu an rantsar da shi a karo na biyu, bayan shekara takwas da shan kaye a hannun Nana Akufo-Addo.
A jawabinsa na karbar mulki sabon shugaban ya yi alkawarin dawo da martabar tattalin arzikin kasar.
Da kuma manufar tattalin arzikinsa mai tafiya babu kakkautawa ba da ake kira ’24 hour economic policy’ mai cike da takaddama.
Shugabannin kasashe 21, ciki har da shugaban Najeriya da Ecowas, Bola Tinubu ne suka halarci bikin rantsarwar.
.