An kone wata mota da ake zargin mallakar ƴan sanda ce a Garko, Jihar Kano, bayan arangama da ta barke tsakanin jami’an tsaro da mazauna yankin.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan wasu mutane da ake zargin masu fashi da kisa ne suka kashe wani mai babur, Umar Idris, ɗan kauyen Kamfa.
An ce wadanda ake zargin sun tare marigayin ne a kan hanyarsa daga garin Buda, suka sassare shi sannan suka kwace masa babur dinsa, kirar Bajaj.
Bisa ga bayanan da aka samu, al’umma da abokan sana’ar marigayin sun matsa lamba kan jami’an tsaro da su mika wadanda ake zargin domin a hukunta su bisa laifin da suka aikata.
Wannan ya haifar da hatsaniya tsakanin ƴan sanda da mazauna yankin, wanda ya ƙare da konewar motar a harabar caji ofis ɗin ƴan sanda na Garko.
Wata majiya daga garin ta tabbatar da konewar motar, amma ta ce har yanzu ba a tabbatar ko motar ƴan sanda ce kai tsaye ko kuma ɗaya daga cikin motocin da aka ajiye a ofishin ba.
Kakakin rundunar Ƴan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce rundunar na ci gaba da bincike kan yadda lamarin ya faru, tare da tattara cikakkun bayanai.
