
Shafin Haramain Sharifain ne, ya tabbatar da wannan sanarwa, yayin da aka ga jinjirin watan a wurare daban-daban na ƙasar.
Hakan na nuni da cewa azumin bana zai fara a ranar Asabar, 1 ga watan Maris, 2025 a kasar da sauran kasashen duniya.
Wannan na nufin cewa Musulmai a Saudiyya za su fara azumi a ranar Asabar.
Aminiya ta rawaito cewa, kasashen Qatar da Oman sun sanar da cewa za su fara azumin Ramadan a wannan ranar Asabar.
A yayin da ake shirin shiga wannan wata mai alfarma, an yi kira ga Musulmai da su yi amfani da lokacin azumi wajen ƙara yawan ibada, yin kyawawan ayyuka, da taimaka wa marasa galihu, duba da yanayin tattalin arziƙin duniya.
Tun ranar Alhamis Mai Alfarama Sarkin Musulmi Sa’adu Abubakar ya sanar da dubana fari na jinjirin a yau Juma’a, ana kuma jiran sakamakon duban nan da ‘yan awanni .