Yajin aikin wanda ya jefa al’ummar jihohin Kaduna, da Zamfara da Sokoto da Kebbi cikin halin rashin wutar lantarki na tsawon kwanaki biyar, na da nasaba da korar ma’aikata sama da 900 da kungiyar ke zargin kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna ya yi ba bisa ka’ida ba.
A zantawarsa da wakiliyarmu Hafsat Iliyasu Dambo, shugaban kungiyar ma’aikatan kamfanin wutar lantarki na Kaduna kwamared Ummaru Lawal Aliyu yace sun janye yajin aikin ne sakamakon Shiga tsakani da gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya yi.
Kwamared Ummaru yace a halin yanzu an dawo da wutar lantarki a jihohin da abun ya shafa yayin da zasu ci gaba da zaman sulhu domin ganin kowane bangare ya samu adalci.
