Ƙungiyar Ma’aikatan Sufuri da Masu Aiki a Tasha (RTEAN) reshen Jihar Kano ta dakatar da shugabanta na tashar Kwanar Dawaki C, Auwalu Bello Ismail.
Wannan na cikin sanarwar da Sakataren Kuɗin ƙungiyar, Muhammad B. Abubakar, ya fitar a ranar Juma’a 24 ga Oktoba 2025.
Sanarwar ta bayyana cewa an dauki matakin dakatar da Auwalu Bello ne sakamakon ci gaba da bayyana kansa a matsayin shugaban RTEAN na Kano duk da kasancewar yana ƙarƙashin wani sashe na ƙungiyar, abin da ƙungiyar ta ce ya sabawa dokokinta.
Ƙungiyar ta ce dakatarwar ta fara aiki nan take tare da umartar Auwalu Bello ya mika duk wani abu mallakin ƙungiyar da ke hannunsa zuwa babban ofishinta na jiha.
