
Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ta dakatar da masu gabatar da kara biyu, sannan ta gargadi wasu alkalan kotunnan shari’ar musulunci biyu bisa laifin kin bin ka’ida.
Mai magana da yawun hukumar, Baba Jibo Ibrahim, ya tabbatar da wannan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
A cewar sanarwar, hukuncin ladabtarwar ya biyo bayan zaman taron Hukumar karo na 80 da aka gudanar a ranar 22 ga Afrilu, 2025, bisa shawarwarin da kwamitin karɓar korafe-korafen jama’a na bangaren shari’a ya bayar.
A cikin hukuncin, an dakatar da Ibrahim Adamu, wanda ke matsayin Babban Rajistara na II a Babbar Kotun Shari’a, daga aiki tare da dakatar da biyansa albashi na tsawon watanni shida.
Bayan an same shi da laifin cin zarafi da yunkurin kai hari ga wani babban jami’i dake gaba da shi, laifukan da suka ci karo da dokokin hukumar ta 2004 da kuma ka’idojin hukumar kula da harkokin shari’a.
An bayyana cewa wannan shi ne karo na biyu da aka gurfanar da shi gaban kwamitin bincike saboda irin wannan laifi na tada hankali.
An kuma rage masa matsayi daga matakin albashi GL-13 zuwa GL-12, sannan dakatarwa da fara aiki nan take.
A wani bangaren kuma, an gargadi Alkali Mansur Ibrahim na babbar Kotun Shari’a bayan tabbatar da cewa ya yi kalaman batanci ga wani wanda ke gabansa a kotu.
Haka zalika, Alkali Nasiru Ahmad na babbar Kotun Shari’a shi ma aka gargade shi saboda bayar da umarnin tsare wani.