
Daga Aisha Ibrahim Gwani
Likitocin a Indiya sun ciro cokula 29 da, burushin wanke baki 19 na wanke baki , da kuma biro biyu daga cikin wani mutum.
Mutumin daga garin Bulandshahr take, an kuma kwantar da shi ne a wata cibiyar warkar da masu shaye-shaye a Ghaziabad tsawon wata guda.
An garzaya da shi asibiti bayan da ya fara korafin ciwon ciki mai tsanani.
Binciken farko aka yi masa aka gano karafa da abubuwa masu kaifi da yawa a cikin cikinsa.
Hakan ta sa likitoci, karkashin jagorancin Dakta. Shyam Kumar, suka gudanar da aikin gaggawa a asibitin Hapur don ceto rayuwarsa.
“Mai matuƙar rikitarwa da hatsari, domin cire kowanne abu daya bayan daya cikin kulawa domin guje wa lalata wasu sassan jikinsa”. In ji Daktan
Duk da hadarin da ke tattare da aikin, an kammala shi cikin nasara.
A cewar jaridar Hindustan Times, makamancin wannan lamari ya faru a shekarar 2022 a birnin Muzaffarnagar, inda aka ciro cokula 63 daga cikin wani mutum da ke fama da shaye-shaye.
Haka kuma a 2019, wasu likitoci a Himachal Pradesh sun gano cokula da burushi da wuka da kuma makulli a cikin wani marar lafiya da ke fama da tabin hankali.