
Yafiyar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Maryam Sanda da sauran mutane 174 tana kasa, tana dabo.
Hakan ya biyo bayan sanarwar da ofishin ministan shari’a Lateef Fagbemi ya fitar na cewar sai an sake nazari kan afuwar.
Ministan ya sanar a ranar Alhamis.
“Afuwar da shugaban ƙasa yayi, sai an sake nazari akan lamarin sakamakon ƙorafe-ƙorafen mutane da suke yi.
“Babu wanda aka saki daga gidan gyaran hali, daga cikin fursunoni 175 da shugaban ƙasar ya yiwa afuwa, ko waɗanda ya yi umarnin ayi musu sassauci a hukunce-hukunce da aka yanke musu a bisa tsarin doka.” In ji shi.
A makon da ya gabata ne, shugaban Tinubu ya yiwa mutane 175 afuwa
A ciki har da ‘yan siyasa da dilolin ƙwaya, da kuma waɗanda suka aikata kisan wanda hakan ya janyo cece-ku -ce.