Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja, ta ce adadin mutanen da suka mutu sanadiyar fashewar tankan mai da aka samu a yankin ƙaramar hukumar Katcha ya ƙaru zuwa 57.
A lokacin da ya ke tabbatar da adadin, daraktan yaɗa labarai na hukumar Dr Ibrahim Hussaini, ya ce bayaga wancan adadin waɗanda suka mutu, akwai mutane 52 yanzu haka da ke kwance a asibi suna jinya.
A dai ranar 21 ga wannan watan ne aka samu faɗuwar tankan mai a yankin, inda mazauna yankin suka yi ƙoƙarin ɗibar mai sakamakon malalar da ya ke yi, lamarin da ya haifar da mummunan iftila’in.
A lokacin faruwar lamarin, mutane 35 ne aka tabbatar da mutuwarsu, sannan wasu da dama suka samu munanan raunuka maban-banta.
Ana yawan samu faruwar faɗuwar manyan motocin ɗaukar mai a Najeriya, wanda kuma ke janyo asarar rayuka da kuma ɗinbin duniya.
