
Aminu Abdullahi Ibrahim
Shugaban hukumar bunkasa fasahar halittu da bincike ta kasa (NABDA) Farfesa Abdullahi Mustapha, ya tabbatar da cewa irin noma na GMO ko kadan bashi da Haɗari ga lafiyar al’umma.
Ya ce kayan gona da aka samar da su ta hanyar binkice da bunkasa fasahar su wato GMO ba su da illa ga lafiyar jama’a kuma suna da matukar amfani wajen magance matsalar abinci a Najeriya.
Ya ce damuwar da mutane ke nunawa akan GMO yawanci tana fitowa ne daga rashin sahihan bayanai da kuma tsoron abin da ba a fahimta ba.
Farfesan ya bayyana cewa hukumar NBRDA na ci gaba da fadakar da manoma matasa da sauran al’umma ta hanyar shirye-shiryen horo da bayanai domin fahimtar amfanin fasahar halittu.
Ya ce babu wani samfurin GMO da zai shiga kasuwa a Najeriya sai an tantance shi sosai kuma hukumar NBMA ta amince da shi.
A cewarsa GMO na taimaka wa manoma wajen samun karin amfanin gona rage kwari da cututtuka da kuma jurewa sauyin yanayi.
Ya kuma jaddada cewa GMO ba zai maye gurbin noma na gargajiya ba sai dai zai kara karfafa shi domin inganta rayuwar manoma da tabbatar da wadatar abinci a kasar nan.