Madugun darikar Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf, a matsayin amintacce, wanda ya shahara wajen biyayya tare da gudanar da shugabanci na gari.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne ta cikin sanarwar taya gwamna Abba Kabir Yusuf murnar cika shekaru 62 a duniya.
A cewar Kwankwaso gwamna Abba Kabir Yusuf ya taka rawar gani kan ci gaban al’umma tun daga lokacin da yake mai taimakawa gwamna, har ya zama kwamishina, yanzu kuma yake matsayin gwamnan Kano.
Kwankwaso ya kara da cewa a kasa da watanni 19, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya fasalin Kano ta hanyar fito da sabbin tsare-tsare da ayyukan da suka ratsa sassan jihar.