A yau Litinin 25 ga watan Nuwanba ake bikin ranar yaki da cin zarafin mata a duniya.
Majalisar Dinkin Duniya ce ta ayyana wannan ranar domin tunawa da irin mawuyacin halin da mata ke fuskanta sanadiyyar cin zarafi da tsangwama da ake yi musu a duniya.
Bikin ya samo asali ne a shekarar 1960 lokacin da wasu mata ‘yan uwan juna da ake kira Mirabal Sisters suka mutu a fafutukar neman yancin mata a kasar Dominican Republic.
A nan Nijeriya da kuma Kano matan na fuskantar irin wannan matsala, inda aka samu rahotanni cin zarafin matan.
Matsalolin da matan suka fi korafi a kai sun hada da fyade, barazanar aure, da wulakanci a wuraren aiki da sauransu