
‘Yan sanda a jihar Michigan da ke Amurka na gudanar da bincike a kan kisan aƙalla mutum huɗu da wani ɗan bindiga ya yi a wata coci da ke jihar.
Har yanzu ana jin cewa akwai mutanen da suka ɓata, ba a san inda suke ba.
Ana zargin wani tsohon sojan ruwan ƙasar ne ɗan shekara arba’in ne ya kai harin yayin da ake tsaka da ibada, a inda ya danna cikin cocin da motarsa, daga bisani ya cinna mata wuta da kuma yi harbin kan uwa da wabi kan taron masu ibada.
Jami’ai tsaro sun isa wurin mintuna kaɗan da faruwar lamarin, sun kuma yi nasarara kashe shi a musayar wutar da suka yi da shi, kodayake har yanzu ba a san dalilinsa na kai harin ba.
Rahotanni sun ce karin mutum takwas sun jikkata sakamkon lamarin yayin da hudu suka mutu.
Gobarar da ya haddasa ta ɗauki tsawon sa’o’i kafin a iya kashe ta, lamarin da ya sa cocin ta ƙone gaba daya.