Shugaban hukumar NDLEA mai hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, Birgediya Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya, ya ce hukumar ta kama mutane fiye da dubu goma sha takwas da dari biyar da ake zargi da tu’ammuli da miyagun ƙwayoyi a 2024 da muka yi ban kwana da ita.
Ya kuma ce NDLEA ta ƙwace haramtattun ƙwayoyi masu nauyin kilogiram milyan biyu da dubu dari shida a shekarar.
Bubba Marwa bayyana haka ne lokacin ƙaddamar da sabon ofishin hukumar da gwamnatin Amurka ta gina a jiha a Lagos jiya Talata.
Sabon ofishin, da za a riƙa amfani da shi wajen tattarawa da tantance hujjoji kan muggan ƙwayoyi, ya samu yabo daga shugaban hukumar, inda ya godewa gwamnatin Amurka saboda goyon bayan da ta ke ba NDLEA wajen yaƙi da safarar ƙwayoyi.