Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi watsi da batun soke asusun kula da manyan makarantu,
TETFund.Shugaban kungiyar shiyyar Owerri, dake kunshe da jami’o’i biyar a jihohin Anambra, Abia da kuma Imo, ya ce soke shirin TETFUnd zai baiwa jami’o’i masu zaman kansu damar samun ci gaba fiye da jami’o’in gwamnati.
Da yake jawabi ga manema labarai a Sakatariyar ASUU, shugaban ASUU na shiyyar Owerri, Farfesa Dennis Aribodor, ya ce kungiyar za ta tattauna da majalisar dokokin kasar kan lamarin.